Lyrics

(Amude on the beat) Ah-ah, ayye guda dangi An ce muku ga amarya Ku taho ku raka ni muje yau ne za'a kai amarya In kaga ango na zumudi an dauko amarya dangina Ga amarya (Ah, ahayye) Ga amarya (Sabuwa amarya) Ga amarya (Ah, ahayye) Ga amarya (Sabuwa ango) Ga amarya (Iy-yeah) Ga amarya (Yau ne za'a kai amarya) Rike, bude kunnen ki ga wani dan sako amarya (Amarya) A kace aure da dadi ammah sai kin kula amarya (Amarya) Soyayyar da kin kai mishi sai kin kara amarya (Amarya) Yau ga ki ga shi za'a raka ku gida na aure (Ga amarya) Ah, ahayye duniyar ku sabuwa ango (Ga amarya) Ah, ahayye duniyar ku tayi amarya (Ga amarya) Amarya da ango sai kuyio soyayya (Ga amarya) (Ga amarya) Nace mahassada da kun ji (Da kun ji) Amarya ta wuce maku kun ji? (Kun ji) Watarana sai labari (Sai labari) Yanzu ta riga ku fatan an ji (Aunty amarya) Amarya ta riga ta lula Da kun bari ai kun ji (Amarya ce) Kuma amarya komai zasu fadi bakya ji (Amarya ce) Kuma ma kin yo masu nisa nine na fada kuma sun ji (Amarya ce) Amarya bar kuka kiyo hakuri zaki bar dangi (Ga amarya) Toh kin ji amarya (Ga amarya) Kin ji amarya (Ga amarya) Ki zauna lafiya kin ji amarya? (Ga amarya) Amarya ta ango (Ga amarya) Amarya ta ango (Ga amarya) (Ga amarya) Wai menene aure? Menene aure? Zaman aure hakuri ake bida, ibada ne aure Ki fahimce shi ya fahimce ki shine a zaman aure Ku dauka ku abokai ne wajen zaman aure Kuma lallai-lallai banda boye-boye cikin aure Ki fada mishi mai ke damun ki tun da har kun yo aure Shine mai share hawayen ki hakki a cikin aure Kuma kar kiyo fada, hakuri shine zaman aure dangi na (Ga amarya) Allah sarki amarya (Ga amarya) Allah sarki amarya (Ga amarya) Duniya sabuwa amarya (Ga amarya) Duniya sabuwa amarya (Ga amarya) (Ga amarya) A sa mata lalle (Ga amarya) A sa mata lalle (Ga amarya) Amarya a kai ta a dakin ta (Ga amarya) Tunda tayo aure (Ga amarya) Amarya ku barta da angon ta (Ga amarya) Shine zaya kula ta (Ga amarya) Don amana ce gun sa (Ga amarya) Ki rike amana (Ga amarya) Toh ta kyale dangin ta (Ga amarya) Yanzu kaine dangin ta (Ga amarya) Don Allah kar da ka cuce ta (Ga amarya) Ka tuna komai zaka yo (Ga amarya) Kayo domin Allah (Ga amarya) Allah shine ke baka (Ga amarya) In ya baka ka dube ta (Ga amarya) Don har ta zabe ka (Ga amarya) Toh ka zama uba gun ta (Ga amarya) Karda ka kyare ta (Ga amarya) Karda ka zage ta (Ga amarya) Karda ka duke ta (Ga amarya) Toh kaji nasiha ta (Ga amarya) (Ga Amarya)
Lyrics powered by www.musixmatch.com
Get up to 2 months free of Apple Music
instagramSharePathic_arrow_out