Lyrics

Dan marayan zaki, Allah ke baka abinci Dan marayan zaki, rike ma'aiki ka wuce kunci Dan marayan zaki, yi alwala kaje masallaci Dan marayan zaki, kar kaiwa kowa habaici Dan marayan zaki, waka batasa kai takaici Dan marayan zaki, kai waka kurum da azanci Dan marayan zaki, magana karta hana kayi barci Dan marayan zaki, ga albishir ban tukuici Dan marayan zaki, kara rike Allah a zuci Zauna da lafiya da kowa da wata rana kana makwanci Yiyah, ni na gode sarki Allah bani dogaro a kan kowa ba Kuma na gode sarki Allah ban iya in yaudara ko daya ba Allahu ni ina gode ma ba'a sanni fagen cuta ba Allahu na godema ka ban basira ban raina ba Allahu kai ka amince inyi waka ko ban kyama ba Allah da yardarka munkaje Madina ziyara babba Allah da yardarka anka ganmu koda mutum bai so ba Allahu yanda kaso kakayi ka dauken uwa ban so ba Allahu na godema kyautarda kayine ba wani ba Mahmudu ka bani Muhammadu, sai gasu ban auneba Allahu sa musu soyayyar ma'aiki rabasu da kunci Dan marayan zaki, kara rike Allah a zuci Zauna da lafiya da kowa dun wata rana kana makwanci Eyy ban kida zanyi waka ban zo in zagi dan kowa ba Kaban kida kurum waka zan kai daga jinka ba shirmeba Taken ta in kaji wakar ka san banyo shirin wasa ba Ban danyo zubin wasa ba sannan banyo shirin roko ba Idan kaji tai maka zafi wallahi ba nufi na kai ba Wakar kawai nake waka kuma ba gadona ba Iyakaci in fadi abunda na sani don bazan boye ba Inma ka zageni kaje ka zagi ba zaya fito ba Inma ka cuce ni to cutarka batayi rana ba Da ace wanine ke badawa sai mu rasa abinci Dan marayan zaki, kai waka kurum da azanci Kai mai talla ka dau tallakka wata rana kamar ba kai ba Karka hangi wanda ya fika kace zaka gunsa ba dai-dai ba Rayuwa irin ta duniya wani ya fika wanin bai kai ba Kar kayi gaggawa domin bukata ba zata biya ba Gaggawa aikin shedan haka naji ba ni na fada ba Tsaya matsayinka yaro duniya ba gida na zama ba Ka lura da me kakeyi Allah sa ba haramunne ba Da akwai wata magana da zana barta ban tono ba Kar kai zatonma da kai nake zancenga ni na saba Zana furta zancen domin bam son barinsa a zuciya Dan marayan zaki, yi alwala kaje masallaci Dan marayan zaki, Kar kayiwa kowa habaici Ban niyyar ince komai ba ba kuma don ina tsoro ba Naso in bar kaza a cikin gashin ta ban figa ba Amma na lura wadansu na batu basu san kara ba Wanzami bai son jarfa shi bai so a maida mai ba Matsala ta baki sai ya fada harshen sa bai tauna ba Da an mai da mai sai yaji da tun fari bai furucin ba Da zan bude zancen nan matsayin ka ba zai wuce jaki ba Da zana baje maganar idon kowa ba bakafi kare ba Inda zana tone ko a gidanka baka yi min gurni ba Riga ta mutunci ita nasa in banda hakan da kace Dan marayan zaki, Allah ke baka abinci Dan marayan zaki, rike ma'aiki ka wuce kunci Dan marayan zaki, yi alwala kaje masallaci Dan marayan zaki, kar kaiwa kowa habaici Dan marayan zaki, waka batasa kai takaici Dan marayan zaki, kai waka kurum da azanci Dan marayan zaki, magana karta hana kayi barci Dan marayan zaki, ga albishir ban tukuici Dan marayan zaki, kara rike Allah a zuci Zauna da lafiya da kowa da wata rana kana makwanci
Lyrics powered by www.musixmatch.com
Get up to 2 months free of Apple Music
instagramSharePathic_arrow_out