Credits

COMPOSITION & LYRICS
Farfesan Waka
Farfesan Waka
Songwriter

Lyrics

Ga wata waka bawan zuciya Gadar zare mai girke rigiya Farfesa sai kabi a hankali Koko kazam bawan san zuciya Gantali ko yawon sharholiya Gadar zare mai girke rigiya A rayuwa sai ka bi a hankali Koko kazam bawan san zuciya (Koko kazam bawan san zuciya) Gantali ko yawon sharholiya Gadar zare mai girke rigiya A rayuwa sai ka bi a hankali Koko kazam bawan san zuciya (Koko kazam bawan san zuciya) Ka kadara kayanka suna cikin jaka ta mai tafiya ka rataya (Jaka na mai tafiya ka rataya) Kazo ka dan raba wata nahiya Ba yar sanaya koda ka zagaya (Ba yar sanaya koda ka zagaya) A hankali hakuri karya rabo Kwana kadan sunanka ya kewaya (Kwana kadan sunanka ya kewaya) Shikenan ka koma dan gari Sai ka shagaltu da neman dukiya (Sai ka shagaltu da neman dukiya) A zuciya da akwai wani ba'ari Shine da hakkin tsarkake zuciya (Shine da hakkin tsarkake zuciya) Hanu guda in shirya gadar zare Sunata kuzun girke rigiya (Sunata kuzun girke rigiya) Gaba dubu inka zurma ka mula A duniya ka koma mujiya (A duniya ka koma mujiya) Hali guda hudu in baka barsu ba Zaka dade a cikin hauragiya Ga wata waka bawan zuciya Gadar zare mai girke rigiya Farfesa sai kabi a hankali Koko kazam bawan san zuciya Hali na tsaro halin dan kare Dan kwaikwaiyo dan bashi da zuciya (Dan kwaikwaiyo dan bashi da zuciya) Halin biri barna mamagunciya Ga baida tsaron mai masa tarbiya (Ga baida tsaron mai masa tarbiya) Kaya niki tafiyarsa da kyar da kyar Ga littafa da tilin kin gaskiya (Ga littafa da tilin kin gaskiya) Tururuwa hadama ga handama Bata gudun wani baccin zuciya Gantali ko yawon sharholiya Gadar zare mai girke rigiya A rayuwa sai ka bi a hankali Koko kazam bawan san zuciya (Koko kazam bawan san zuciya) Duniya dauke ni a hankali Kije dani ki aje ni a hankali (Kije dani ki aje ni a hankali) Domin idanki guda ne tal aka Karki ajeni a gefen chokali (Karki ajeni a gefen chokali) Kwaran-niya mai rai bata bar ka ba Na ruwa bai wa kadoji izgili (Na ruwa bai wa kadoji izgili) A rayuwa sai ka bi a hankali Koko kazam bawan san zuciya Ga wata waka bawan zuciya Gadar zare mai girke rigiya Farfesa sai kabi a hankali Koko kazam bawan san zuciya Allah ka maida mafarki zahiri Ran tahamidi ranar zaqida (Ran tahamidi ranar zaqida) Lunbau rabon kwado na nan a kas Diyar barewa tafi diyar gada (Diyar barewa tafi diyar gada) Badon cikin ruwa ban bashe shi ba Abin a kilance ne ko a da (Abin a kilance ne ko a da) Farfesan waka luguden batu Arangamar yaro bisa tukuba Gantali ko yawon sharholiya Gadar zare mai girke rigiya A rayuwa sai ka bi a hankali Koko kazam bawan san zuciya Ga waka sabanin hankali In hankalin bai kai nisanta ba (In hankalin bai kai nisanta ba) Azarbabi na biyewa zuciya Mutum ka lura bazai fishe ka ba (Mutum ka lura bazai fishe ka ba) Idan kabi ta da so, ta kada kai Domin kana bautar marar martaba (Domin kana bautar marar martaba) Son zuciya ne bacin zuciya Madindimi a cikin barababiya (Madindimi a cikin barababiya)
Lyrics powered by www.musixmatch.com
Get up to 2 months free of Apple Music
instagramSharePathic_arrow_out