Lyrics

Rub Master Jarabta da soyayya zafinta na dandana matuka Hakika da kuna gun kaifi ko tasha gaban su wuka Nayi wutar ciki, nayi bakin ciki na share kukana Na shiga can ciki, takai farmaki ta kama hanjina Dakyar nake fidda numfashi, so ya toshe kirjina Wataran kamar inyi ihu ko wani zai gane takaicina Mashi ya sokeni, wa za ya dubeni? Radadinsa zafin azabar ya zarce tunanina Cikin kawaye nake ko barci zana kwanta Na yafe cin amanar da yai mini ya za ai na manta In so ya dukeka, yayanka har jika Bazaka manta ba ya shiga tarihinka kenan So-oh-oh In na mutu shine sanadi ku shedeni Kora da hali, izayar so yamin rauni Fahimta a fuska sone ya cuceni Zaton da nake sabon da mukai zai kwaceni Ninaga takaina so ya tashi kadani Cikin wani rami mai zurfi ya jefani A'a har na tsani labarin da ya shafi soyayya Domin taji min ciwo zuciya tana jinya Na rintsa ido kanso bana ganin hanya Muna tallafar juna a tsakani mun shirya Ganina shi zai auren babu jayaiya Na kori samari kanshi ya rusa tsarina Shikuma Gaskiya daya ce a sanina Ku tsaya kuji al'amarina Ko dan karami a kanina Zaiji an rainan nazarina Wanda nake so shi ya kirani yace wai an sanya masa rana Za ai masa auren dole a dan haka dole muyo bankwana Zance daga bakin wanda na soshi tamkar ma in zauce Na kama tunanin ko nice wai koma ba nice ba Na dau darasi na kama jikina Amma kuma al'amarinnan na damuna Zanso inji menene laifina Banda sukuni har sai mun tattauna Na kure nazarina A iya hangena Ba fadan laifina Kada so ya guje min
Lyrics powered by www.musixmatch.com
Get up to 2 months free of Apple Music
instagramSharePathic_arrow_out