Lyrics

Umar m Lawal zamanga Ya Allah ka iya mana ba dan mu ba Haba kai, iye Toh nagode Zamanga on the beat Ya Allah kama mana Duk matsala ka kawar mana Idan tazo ka tare mana Ai jifar ta wuce bamu san anyo ba Ta wuce bamu san anyo ba Ya Allah kama Allah kama mana Munafukai ka tare mana Mahassada ka tsare mana Kullin su war ware mana Suyi haushin su gama bamu san sunyo ba Allah sarki kainuwa Kainuwa Ta rayu saman ruwa Bata san ita ce aka cewa dashen Allah ba Haka tantabara take Ita ko a ina take In ta tashi da fiffike Hankalin ta gida yake Makwancin nata a nan yake Bata san sunanta uwar alkawari ba Abun sha'awa a gurin damo Cikin natsuwar sa ya kan zamo Yan yaran mu su kinkimo Su jagula shi ya sallamo Da kawaici haka ya zamo Bai san ana kiran sa damo sarkin hakuri ba Mu dauki dabi'un shamuwa Sam-sam, bata da damuwa Ba a yi tayi ramuwa Sai gun yankata bazata ki yin kuka ba Eh Zamanga Ku lura abun da nake nufi Hakuri baya zama dafi Ko an ma mugun nufi Shi sara bai hana gamji yayo toro ba Kai dai rike hakuri Rike shi ya zama guzuri Koda za kaga jinkiri Duk mai ha'ka ba zai gaza cinma ruwa ba Haba Ya, Allah gyara mana Duk nasara kawo mana Kar dama ta wuce mana Mai kushe mu ba zaya ga yadda yaso ba Kai mai zinde Kai mai zinden baka Toh mun yi riko da إِذَا وَقَ Har يسٓ da تَبَٰرَكَ Mun zama turmi sha daka ko baka so ba Haba Nagode Umar m Lawal zamanga On the mix Zamanga
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out