Lyrics

Maimuna gimbiya ina baiwar Allah? Dadin duniya kina nan da kamalah Giwa ko ana matsi sai kin walah Maimuna mun yabe mai jimirin sallah Maimuna ba musu irin ƙila wa kala Maimuna kin kula da sunnah da farila Maimuna bangaren zumunci mu'amala Maimuna ce baba 'ya gun babba Mai halayen kwarai mun duba Maimuna hasadar magau ta zama taki Maimuna kin ji kin ji jita ta kira ki Maimuna taimakon mutane a jininki Maimuna ki ta kwaliya ga kayan ki Maimuna kinyi kyau a mota haka doki Maimuna dole zana fassara sunanki Mai albarka a dan duduba Larabci ne bazamu kiyi ba Wanan tamburan muna yinsa ga Maimuna Yar birni tana ta turanci Maimuna Mai hakuri ta nada imani Maimuna Ji da ado adon gari kece Maimuna Mai kamshi a koda yaushe ce Maimuna Kunshi yafi kyau da hanayyen Maimuna Zaga gari baiwar rabva Nasarori ai basa kare ba Mai tafiya kazo da sako in baka Ga jita tana ta tashi sam barka Ga yara suna rawa 'yan albarka Ga manya sunata kirgida kai haka Allah yai ruwa manoma na shuka Ko ni ya kamata wakar in taka Wakar Maimuna bazan fasa ba Maimuna ai kina da suna babbah Ki shagalinki duniya a amfana Duk dangi da 'yan uwa kowa murna Sanan lafiya da kowa kin zauna Har aljana zaki aiki ya nuna Maimuna gimbiya da kyauta da amana Kuma kuka na duniya sai kin daina Yar manya matar manya Nasarori ai basa kare ba
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out