Similar Songs
Credits
PERFORMING ARTISTS
Ali Jita
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Abubakar Adamu
Lyrics
PRODUCTION & ENGINEERING
Abubakar Adamu
Post-Production Engineer
Lyrics
(Sultan with the beat baby)
Ga sako ina fada
Ku fahimta mahassada
Indai lokacin kane
Nasara ba zata barka ba
Ga abu nan a zahiri
Kuje ku fada gari-gari
Jirgin duhu bai bari
Wasu ne basu gane haka ba
A gun Allah nake bida
Rai na shi ya da dada
Ya yarje na shimfida
Haushin ku ba zaya kai ku ba
Ga magana a hankali
Makaranta ko a dandali
Hannun mu yana da cokali
Mu dangwala ko ba da son su ba
Toh har yau gamu nan tafe
Da ƙafafu babu rarrafe
Waka zamu wallafa
A ji dadi ba za'a ki ta ba
Bauna saniyar sake
Zaki na gurin rake
Ya wani zai fututtuke
Yayi ta fushi shi ba uban mu ba
Yanmata yaya za ayi?
Ko kin shaida saurayi?
In da kudi yazo ayi
In kuma babu ba za'a bashi ba
A taure mai kamar kare
Maganar zamu warware
Mune ke ta jan zare
Don waka ba za'a fimu ba
Kura mai yawan kwadayi
Ba a son ta ko da dai
Abu zancen mu ɗai da ɗai
Gwarawa basu gane kanshi ba
Timbele ga tunkiya
Nono sai ga saniya
Mai son jarumar diya
Ba zai ce, "Bai zo da Abu ba"
In nayi batu a zahiri
Dan kauye da dan gari
Ga sanda ta zunguri
Mai yawo ba zaku gan ta ba
Ni nagode wa Rabba na
Yayi baiwa na adana
Na guji duk abin tsana
Tarihi bai zo da aibu ba
Soyayya nake nufa
Ciki ba a rufa-rufa
Kar wani da ya zurfafa
In ba a gane asalin sa ba
Magana ce da korafi
Gun makiya da hadafi
Sai yai ta kan su zaya fi
Ba tilas sai sun biyo mu ba
Hutu ba na karuwa
Juya bata haihuwa
Aure inda gurguwa
Bai dace da a kaita nesa ba
Yau mune da lokaci
Mun tserewa firgici
Nasarori muke ta ci
Har abada ba zamu fadi ha
Gun Allah muke bida
Su boka suke fada
Sun ce, "Za ya da da-da"
Ni nace, "Ba zaya kar mu ba"
Lyrics powered by www.musixmatch.com