Lyrics

A'a Adamu Zango a fagen fama (ja muje) Na kira na hagu, hagu dama (ja muje) Mai kida na du'a Yeah yeeh Mai kallo gami da mai sauraro kuji ni Zan yo waka ta Hausa ba ta dabo ba Zancen darajar mawakan Najeriya Musamman na Arewa zan bayyani babba Dangi yan uwa na Hausawa su suka yada mu Toh ya baza muyo kuka ba Sun maishe mu saniyar ware Bamu da kima a idanun su sai kace wata dabba Koh aure fa basu baiwa mawaki (ja muje) Sai kaji sun kira shi ma da maroki (ja muje) In ka matsa su sa a baka na jaki (ja muje) Amma in biki yazo ko wakar siyasa Ko birthday 'yar su zaku sha mamaki (ja muje) Sai su kira ka don ka burge baki (ja muje) Kai ta kida kanata washin baki (ja muje) Su ko suna rawa da takun shoki (ja muje) Suyi kwando su ringa maka liki (ja muje) Sun maishe mu duka 'ya'yan tsaki (ja muje) Toh idan nayi karya kuzo ku bani amsa Waye gwanin su sai kuyi duba Sun dauka waka shirme ce ganina Ni ko gareni gata babba Nagode wa rabbana mai iko Yayi min baiwa Zango ni bazan raina ba Wani yayai dogaro da aikin ofis Wani sai yaje kasuwa ya irgo riba Rufa laya wanan abarwa walunku Wanda yayai shuka ya jira ta za yayi girba Kiwo yafi kyau gurin makiyayi Mai hakuri shi zaya jure tsumaye Mai neman lakan sa yafi baraye Kar kuyi jinkiri ku bini a sannu, sannu Zanayo tankade nawa nayi tsaba Haka a fuska sai ku ringa yaba mu In a kai gefe zuciyarku na tababa Wasu na kin mu sanadin sana'ar mu Sun fi so mu mace ma kawai suzo suci kunba Duk mai gaskiya a rai bai shayi Ko kuma so kuke mudinga bulayi In dai naka, nakane kan mu zo ku nuna kishi Mu kula da kan mu kar muyi zanba Muda muke abin azo a yabawa Mu ake warewa asa sahun mabarata In dai takamarka Hausa kake yi To kaje hausar taka mu muke yadawa Zalinci da baki sai mu hana shi Kana muke yin gargadi gurin mawatada Wanda yake zubi ya dauki adashi Mai rabon dacewa yazo ya bamu mukata Kai lamarin bahaushe nada takaici (ja muje) Gunku mukai zuma ku kubamu madaci (ja muje) Nesa ku kai ruwa ku kyale makwabci In mun ja bakin mu, zamu fasa ne Wanda bai ganewa lalai yasa mu fahimta Wasu kuke zara kuke goyawa In mukai wakar Hausa tamu bayka san ta Inda zaku tsallaka yankinsu Nasu ne nasu akasin sa basa ranta Kai kuma kadabi sai kayi huce Mu kuma bamu so a raina matsince Kuyi gyra kar lokaci ya kurewa Kar kuzo gunmu muce bazamu iya ba Waka sai da ilimi aka yin ta Kuma baiwa ce hikima tazo daga rabba Allah duk wanda yaso za yayai waka Tasa kyautar bai duba karami ko babba In yayai maka sai kazo da tinani Wanda ko mai digiri a kai bazaya iya ba Ni bazan yi takamar masters ba Tinda wanda ya bani bai yi min gori ba Wai wani dukiya yake juyawa (ja muje) Dan boko yana ta bubudawa (ja muje) In baka zo guri su ka saucewa (ja muje) Allah ne kadai abun kamawa Wanda kaska tai aba dan bazata kure ba Ya boye sani na gaibu agu ne Aljani koda dan adam bazai gane ba In yayai wa wani abinda yake so Digiri, tarin dukiya baza suyi ma ba Dan haka yan uwa ku dinga tinawa Kar mubi zuciya dake hana karwa Ba dan rabbi keyi ba ni na fahimta Dan baru shi bazai motsa ba
Lyrics powered by www.musixmatch.com
Get up to 2 months free of Apple Music
instagramSharePathic_arrow_out