Top Songs By Nura M. Inuwa
Similar Songs
Credits
PERFORMING ARTISTS
Nura M. Inuwa
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Nura M. Inuwa
Songwriter
Lyrics
Eh matata ce ko kwa 'ya ta?
Bakon lamari a rayuwata
Yazo min banyo zato ba
Gani ina auren 'diyata
Ah mijina ne shi ko Ubana
Bakon lamari a rayuwata ta
Yazo min ban tsallake ba
Gani ina auren ubana
Mata ko 'ya sai ku duba
'Ya dai da uba babu aure
Bakon lamari inya taso
A shiga hali matsananci
Eh nashiga tsanani a rayuwata ta duniya inane ni zan sanya kaina
Aure ne dan raya sunna da kyan niya zaya zaman baci na suna
Duk mai rai bai iya haurewa 'kaddara mu dinga tunatarwa da juna
Yanzu ina zanje na kwana? A ce miji nake a idanu na 'diya ta
Mata ko 'ya sai ku duba
'Ya dai da uba babu aure
Bakon lamari inya taso
A shiga hali matsananci
Eh so mai saka yayi 'dauri dabai-bayi ya kai ni ga auren ubana
Babbar matsalar da nai shigewa itace harma da ciki nai jikina
Dan dayake yawo jikina idan na haihu yazama 'kane kokwa 'dana
Ga mutuwa dai ba a santa amma a yau ni ita kaina nakewa fata
Mata ko 'ya sai ku duba
'Ya dai da uba babu aure
Bakon lamari inya taso
A shiga hali matsananci
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'unn Allah sarki na duba
Al'amarin nan daya taso ya faru ne bada sani koda so na rai ba
Amma yazo dole kuka idaniya bansan yaushe zaya kau ba
So na iyaye dasu da 'ya'ya
Amma a yanxu sai nafi so in bata rata
Mata ko 'ya sai ku duba
'Ya dai da uba babu aure
Bakon lamari inya taso
A shiga hali matsananci
Eh nama tsani duniya gabadai
Idan da rai yazanyi da 'yan sa ido da kallo?
Ga kuma cuta ta laulayi in ta tashi ko gaban jama'a zana hau kumallo
Zo kuga mata kuma 'ya a gurin ubanta koda sai ai ta jefa 'kwallo
Wayyo ni inta rausa kuka
Ina tuna nayi asarar rayuwata
Mata ko 'ya sai ku duba
'Ya dai da uba babu aure
Bakon lamari inya taso
A shiga hali matsananci
Buri na uba inya haihu yasamu 'ya da ta tasa yayi mata aure
Nima da hakan a rai na, nasamu 'ya na bata miji suyi zaman su tare
Yau matsala ta shigo jikina tai tabo da ban iya gogeshi ko na sare
Na riki 'ya ta zama na aure
Yanxu ma idanuna na gudun su ganta
Mata ko 'ya sai ku duba
'Ya dai da uba babu aure
Bakon lamari inya taso
A shiga hali matsananci
Eh ni 'ya ce wadda aka haifa da aure amma kuma yau nai daban da saura
Domin sauran suna da dama na rayuwa da zasuyi ba tsangwama harara
Allah masanin zahiri na da badini komai a garan kai ka tsara
Kawon 'dauki na daina fama
Dan gani zaune na rasa 'yanci irin na mata
Mata ko 'ya sai ku duba
'Ya dai da uba babu aure
Bakon lamari inya taso
A shiga hali matsananci
Eh mata tace kokwa 'ya ta?
Bakon lamari a rayuwata
Yazo min banyo zato ba
Gani ina auren 'diyata
Mijina ne shi ko Ubana
Bakon lamari a rayuwata ta
Yazo min ban tsallake ba
Gani ina auren ubana
Mata ko 'ya sai ku duba
'Ya dai da uba babu aure
Bakon lamari inya taso
A shiga hali matsananci
Lyrics powered by www.musixmatch.com