Lyrics

Nagane, so ginshikin komai ne yanzu tilas ne Nayi kira,mu rike hakan zamuyi dace na alkhairi Farko sai nasa rabbi wanda shi ya halicci soyayya Yasata a ran kowa saida ita muke tafiya Tazama ginshikin komai, in bata ba lafiya Rokonka nake rabbi kashen a kan soyayya Soyayyar Allah, da manzon Allah sai ahlul baiti Wanda yayi rashinku bashi kan hanya Ita soyayya bata haifar da komai, sai alkhairi Saboda ita yake zuwa, komai yazamo cikin tsari Itace mai sa fuskoki su kasan a cike da annuri Muyi dan Allah, zamu zamo a cikin masu babban jari Allah ka cika min buri Zuciya sam ba sharri Dan kar wani yayi min gori A yau na wake soyayya In kunji hayana, duba wurin kuga ko da soyayya In kunga ana kisa, na tabbata rannan babu soyayya Sabama Allah ba'ayinshi idan da soyayya Rikici na kasa, bai tasiri idan da soyayya Manya basu son kanana Suma kananan basu sin manya Mai kudi na gudin talaka Kaga anan sam babu soyayya Soyayya ce mai hada aure ango shida amarya Itace mai chanza hali mummuna kan hanyar gaskiya Har ni kaina nasamu ne sanadinta a yau ina godiya Nagode miki soyayya, usuli na zuwana duniya Allah sarki, wanda shi halicci dukanin duniya Sarari na samaniya, harma kassai dukansu baki daya Duka domin Soyayyar dayakewa manzonsa mai juriya Dukanin duniya, Allah yafi sonsa akanmu baki daya Da ba soyayya, samuwar babu batunshi sam ko daya Alfarmar Annabi, muke shan iska nan cikin duniya Nagane, so ginshikin komai ne yanzu tilas ne Nayi kira, mu rike hakan zamuyi dace na alkhairi
Lyrics powered by www.musixmatch.com
Get up to 2 months free of Apple Music
instagramSharePathic_arrow_out