Lyrics

Uhm hum Uhm hum Uhm Ina ma da arziki masoyi ya san dai yana da gata nai Ina ma da ilimi in dosar da mai so halin ma'aiki ne Ina ma da tausayi masoyi in yafe shi dukka laifi ne Ina ma ina da sai arewa basa kushe tasu baiwa ba Ina ma da maganin na baiwa masoyi ya korai cuta tai Ina ma da dukiya na badda wa mai san rufin asiri na A cee zan fada aji masoyi bazai tauye masu nema ba A ce zani aikata a ko ya ba a kushe masu gyara ba Idan zan fada a ji masoyi bazai zagi shugabanni ba Ina ma da dan saki masoyi da yunwa basa ga juna ba Wasu mafada oyoyo Baba Buhari kudi suka nema Wasu mafada oyoyo na yi dan dada suna suma Wasu mafada oyoyo ba dan kishi suka fada ba Buhari ya zama abin tallata hajjar wakar kowa Buhari ya zama abin kushe an ce ya hana kowa Wadansu suna ta fadin dama ya mutu ya zama gawa Buhari ake zargi ya hana yin safarar shinkafa Kai mu dauka eh haka ne toh minene laifin sa Buhari Toh mu tambayi kakanni kasar mu a da an san ta da noma Kasashe sunfi biyyar wanda mukai wa silla suka girma Ashe gyaran kayanka bai zama sauke mu raba lau ba Wadansu mu basu iri su koma chan a kasar su su noma Da shi suka chi suka sha kuma suyiwa kasa tasu hidima Ni abun da nake tsoro ba saukar sa a miliki ne ba Ni abun da nake tsoro ba wanda zai maye gurbi ne ba Mun shiga kunchi bara ana ta kashe mu muna dada buya A bi mu wurin bauta A bi mu gida a kashe mu da 'ya'ya Muna ta dua'in Allah chanja yanzu da chanji yazo Muke ta farin zanche Muzama kamar kambu suka murzo In munka butulcewa Allah kamar an bamu gumurzu Shin mun gode kenan Kokuma mun kyauta kenan In Allah yayi fushi Mu san da sani mune muka jawo Wake da sannin gaigu Ko zance na akwai aibu? Wasika zuwa ga shugaban kasa Wasika zuwa ga shugaban kasa Mai tsaro mai tsoro a tsakar sallami koda an ce ya bar kasa Wasika zuwa ga shugaban kasa A kaga tudun da ka hau da kyal mu sauke ka sai dai wanda yai kasa Wasika zuwa ga shugaban kasa Wanda yayi ka mutum mai jama'a ne ya nufa kayi shugaban kasa Wasika zuwa ga shugaban kasa Ba shirka kayi ba a hawan ka dalillin nan bai sa ka sha kasa Wasika zuwa ga shugaban kasa Wadansu suna tsafi Wadansu suna addu'a Allah sa ka sha kasa Wasika zuwa ga shugaban kasa Kasake rike Allah toh Baba akwai nissa hanya ta gaskiya Wasika zuwa ga shugaban kasa Kasake rike Allah Baba da da che duk zance na gaskiya Wasika zuwa ga shugaban kasa Cikin masanaantar siyasa akwai ma bida naisa tazo kusa Wasika zuwa ga shugaban kasa Cikin masanaanta ta waka mai badi naisa tazo kusa Wasika zuwa ga shugaban kasa Nufin sa kawai wai shugaban kasa ya kame duk mai da kudin kasa Wasika zuwa ga shugaban kasa Bayan masu kudin ka basu toh in an kame su shin wa ya rasa Wasika zuwa ga shugaban kasa Kunga fadan giwa guda biyu biyawa ke wahala tazam kasa Wasika zuwa ga shugaban kasa Roki illahu ya basu su bamu mu baiwa na naisa mu baiwa na kusa Wasika zuwa ga shugaban kasa Ya Allah kare shugaban da duk bai da niyyan sace kudin kasa Wasika zuwa ga shugaban kasa Allah kare shugaba mai san gyaran tattalin arzikin kasa Wasika zuwa ga shugaban kasa Allah kare Naziru Sarkin Waka mai san yaga chigaban kasa Wasika zuwa ga shugaban kasa Chigaban kasa Allah ka kare musulmai da musulunchi baki daya, amin Ubangiji ka bamu ikon gyarawa kasa mu zama masu godemaka, amin
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out