Lyrics

Ga amarya na ganki amarya Daina kuka gidan bikin kine kin ji amarya Ga amarya na ganki amarya Daina kuka gidan bikin kine kin ji amarya Da sallama farko na kira ka sarki na (ango) Kai kayi min baiwa kice a baki na (ango) Dado salati ya Rabbi gun habibi na (ango) Shugaban bayi shi ka bai wa ceto na (ango) Nasa Sahabban sa sune sillar mutane na (ango) Da Auliya'ulLah masu gyara zance na (ango) Ga amaryar next level amarya (ango) A next level yayi auren amarya mai baiwa Ga amarya na ganki amarya Daina kuka gidan bikin kine kin ji amarya Sha sha'anin ki amarya lokacin kine wannan (ango) Sha sha'anin ki amarya ba yake a wakar nan Ku tashi dake da ango lokacin kune wannan (ango) Aure rahma yau za'a kai ki dakin nan (ango) Ku tashi muje, muje, muje bikin yar gata (ango) Ku tashi muje, muje, muje bikin yar gata (ango) Da soyayya aure yake yin rana (ango) Don Allah ango ka samu dama Ga amarya na ganki amarya Daina kuka gidan bikin kine kin ji amarya Ango daure, takwara na ga shawara (ango) Karbe ta amarya, na santa akwai tarbiyya (ango) Sannan ga bacci, bata sauri gun sauke miya (ango) Toh karda ka bata rai don Allah ku zauna lafiya (ango) Soyayya dadi ta kere wa gishiri na miya (ango) Kyakkyawa ango, don Allah karda kayo gajiyah (ango) Nayi farin ciki sosai ka dace amarya (ango) Amarya ta iya soyayya amarya Ga amarya na ganki amarya Daina kuka gidan bikin kine kin ji amarya A gidan duniya ake, ake, ake aure (ango) A gidan amarya mataye ne suke jere (ango) A gida amarya can ne ake rufo kyaure (ango) Angon amarya, kuna shirin zama tare (ango) Dangi na amarya naga suna tasa turare (ango) Kuyi addu'a, Allah hana su su ware (ango) Ga amaryar next level amarya (ango) Daure amarya ki nuna soyayya Ga amarya na ganki amarya Daina kuka gidan bikin kine kin ji amarya Ku mu gaida MC na gida Malam Ibrahim rikirkita su cikin gida (hayya) Baban Muhammad ka zaga gida-gida Shahrukh Khan gidan bikin ka gargada Ayya, ayya, ayya sai malam (ango) Ayya, ayya, ayya sai malam (ango) Amarya kai tace tana so a kawo Abdul D One ni kuna in wake amarya Da ango Nagode Ga amarya na ganki amarya Daina kuka gidan bikin kine kin ji amarya Ga amarya na ganki amarya Daina kuka gidan bikin kine kin ji amarya Ango
Lyrics powered by www.musixmatch.com
Get up to 2 months free of Apple Music
instagramSharePathic_arrow_out