Lyrics

A cikin mata ba kamarki na duba Kece fitilar wanke zuciya mizani A cikin samari ba kamarka na duba Kaine fitilar wanke zuciya mizani na A cikin mata ba kamarki na duba Kece fitilar wanke zuciya mizani Zuciyata gaba dayanta nabaki Na amince duk inda kike zan biki Kinji sunce da anganoni anganki To kice musu nine cikin mafarkinki So da dadi kamar zuma da alkaki Kinga haske ke maganin duhu Shi masoyinka bazai saka ka tozartaba Makiyi shi kuma baikima ka tozarta ba Duk da kauna kabani naji to na karba Na amince to ka kaini kan mataki babba Inda rai da rabo 'ya'yana zasu cema baba Zanji dadi in har dani dakai zan zauna Naji sanyi a zuciya tabar shan wuya Ina waiga banganki ba nakan tambaya Naji ance soyayya tazamo manuniya In babu ke ki tabbatar ina rijiya Gyara zama mu raya zantukan zuciya Dan mu gano abunda ke cikin zuciya Na gamsu kauna tana saman dukiya, ahh Nima na shaida fanin kauna ai kayi komai Farin ciki kasa shi cikin raina Kayi mai-mai Ja ragamin linzamina mu tafi kaji jarmai Kashiga raina ni ka burgeni In nayi batan kai kai ke saitani Karkai shakka ga hannu jani Kajajace a bangaren so bakai gudu ba Kece silar dake yayen damuwa In har kana kishi zance ga ruwa Zancen ki a ciki ba wata dimuwa A zaman mu ni dakai na dada nitsuwa Wasu nawa so kirari dan tsuntsuwa Sunyo ragon azance ko mantuwa
Lyrics powered by www.musixmatch.com
Get up to 2 months free of Apple Music
instagramSharePathic_arrow_out