Lyrics

Auta Waziri kuke ji malam Beats Ali's production Farin cikinki shine farin cikina Ki bar gudu na ba inda zana zauna Farin cikinka shine farin cikina Kabar gudu na ba inda zana zauna Kina taba ni Kina yawwan tsuma ni Ina kike ne kawai kirani zani Abar fadi na kice kawai a raina Kin sanya kauna tana yawwan zigani Ki bani dama kawai ki bani soyayya Mu sanya yarda kar ayi mana rauni A kanki ne ma suke ta nuna ki Soka baya gabana ina ta nuna soyayya Farin cikinka shine farin cikina Kabar gudu na ba inda zana zauna Farin cikinki shine farin cikina Ki bar gudu na ba inda zana zauna Idan da hali karka barni dan arziki Kazo mu zauna kai kadai naba lokaci Ina da dama dazana so su ma sai naki Suna ta bina naki yanzu sai tsokaci Kawai ka gano ko wata rana kaje biki Saboda mata ko dan abinci ma karka ci Ina da kishi akanka shiyasa zanaki Awa guda cur idaniya basa ganka ba Bazan iya ba Farin cikinki shine farin cikina Ki bar gudu na ba inda zana zauna Sanki yakai munzalin da ban son fada Ko na fada ma baza'a gane karshen sa ba Ki gane cewa a sanki ni ko ban farga ba Ba zan iya ba da wata in bazan ganki ba Jinin jikina da naki sun hade gu guda Wa zai raba su cikin kasar ga ban ganshi ba A kanki zani duniyar da ba namu ba Indai kina nan nasani bazan bata ba Farin cikinka shine farin cikina Kabar gudu na ba inda zana zauna Farin cikinki shine farin cikina Ki bar gudu na ba inda zana zauna Kaine a dama na baza ka kauce ba Waninka ko yazo bazamu saba ba Kasan da soyayya sai anyi hakuri ma Zama na rayuwa ma ya baza'a saba ba Zan samu nutsuwa ma in kana zama gurin na Farin ciki yakan zo ya bazana gode ba Kawai ka yarda rabbi ya hada ni dakai A lamura na zanso ace kazamto gaba Farin cikinki shine farin cikina Ki bar gudu na ba inda zana zauna Farin cikinka shine farin cikina Kabar gudu na ba inda zana zauna
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out