Lyrics
(Malam6ix)
(Mad)
(Ma-mad oh!)
Jiya malam ya ci kwakwa
Saura kadan na ci ankwa
Babu ruwa ga tankwa
Ga Ali Jaja a hanyar makwa
Tsugunne na kan yi a gefe
In na kafa tanti su jefe
Da sun kitsa in tsefe
Masu son na jike na kyafe
Tsugunne na kan yi a gefe
In na kafa tanti su jefe
Da sun kitsa in tsefe
Masu son na jike na kyafe
Tsire
Ni naga zahirin wuta ga ni
Tsire
Kafin yau da sun raina ni
Tsire
Ni gwagwarmaya ta ratsa ni
Tsire
Na soku da kyau ba mai iya zuge ni
Wahala ba dadi wayyo
Kai mai tafiya juyo
Tilas hakurin koyo
Ko jarka tayi yoyo
Tabbas nai kai kawo
Hankaki na barewa bawo
Har mama tace dawo
Na rarrashe ta na zam dodo
Addu'ar da take mi ni
Ta sa aka san da ni
Ciwon ba magani
Wasan ba dadi babu ni
Zo ki ga danki uwata
Kalli Kanin ki yaya ta
Kanwata yar gata
Na Alhaji ga sana'ata
Tsugunne na kan yi a gefe
In na kafa tanti su jefe
Da sun kitsa in tsefe
Masu son na jike na kyafe
Tsugunne na kan yi a gefe
In na kafa tanti su jefe
Da sun kitsa in tsefe
Masu son na jike na kyafe
Tsire
Ni naga zahirin wuta ga ni
Tsire
Kafin yau da sun raina ni
Tsire
Ni gwagwarmaya ta ratsa ni
Tsire
Na soku da kyau ba mai iya zuge ni
(Promix)
Writer(s): Saeed Sulaiman Iliyasu
Lyrics powered by www.musixmatch.com