Lyrics

Mm, mm, mm, mm Mm, mm, mm, mm Lalala-lalala Lala Auta kece ra'ayina, a mukamin farko (ooh ahh) Auta kaine ra'ayina a mukamin farko (ooh ahh) In na tuna labari domin ke, in baki kisha ko zai dadi A sannu a sannu muna tafiya, inayi maki taki mai dadi Bakimin ba'a auta, kin wuce su auta Ga kyau ga da'a auta, lallai kin taka sa'a auta Cikin bacci, nayi mafarki nasanki Ashe kema kina so na, mafarki ya zamo gaske auta Auta kaine ra'ayina, a mukamin farko Bari kaji sabon suna a soyayya, dazani sama Natsu kaji sabon taken soyayya, dazan buga ma A zuciya kayi kamar wani ingarma, mai sa maza su suma A gareka nayo karatun samu, kaine kace na nema Dan autana, mai kauda takaici na A kowace rana, ban canza maka suna auta Dan adam ajizi, kowace rai na bidar kara Mai wa'azi nasiha yake, ko a ina kaji saurara Shi dan adam iri-iri, wani halinsa akwai gyara Wani gyaran ma baya so, kullum zunubi ya tattara Ya Allah ka shiryemu, da lahira musha gara Allah yasa na aureki, mai tarbiya cikin mata Wayyo kaina, kasa naji wani tsoro Kai magana cikin hankali, har kunne ya sauraro Mai nazari yake gane, nisan tafiyar dan kwaro Almajiri ya dau allo, dan boko kuwa sai biro Soyayyace silar aure, a cikin haka har azo taro Haduwarmu dakai akwai murna, dan nasan nazamo mata
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out