Lyrics

Mafarki na, kece So makaho ne Naga baya gane dan gida Bai gani bai ji Bai gudun ya rufta gargada Masu jirwaye su suke gudun sawkar kuda Hadarin kauna ai kina jin yau karar cida Gaskiyar zance Sanki ya taba min zuciya Mai gani ga kyau tafiyyar ki daya bayan daya Zan zamo bawa korafin ki bana firjiya Duk abun da kike so ki ban umarni zan iya Murmushin kauna Kiyi a gare ni in san mafuta Ai idan gaki da wajen ne ya zando wuta Tunda zafin so ya darar wa garwashin wuta Yaudarar kauna wanda duk yakeyi ya bata Toshe kunaye karda ki bi zancen yan zuga Kin zamo sashen zuci babu ke sai ta buga Kin sani koshi shi yake saka a ci a raga Naga tuta ta zani fara in hau karaga Mun zamo daya kin rike ni tamkar dan uwa Ga misalai kin ginan wurare yar uwa Kullum tunani na auren ki inyi wa maza rata Cikar muradu na kin zama ta daban a cikin mata Abinda ke rai na in mallake ki gimbiyar mata Koh gobe na shirya aure muyo dake manufata Ki bani soyayyar ki nima na baki tawa ki alkinta Shi dan kare kin san harshe ke saka kushe shi Duk wanda zai kawo gulmar raba mu toh ki kyale shi Ki sa a rai lallai saye martabar ki nayi al washi Kullum tunani na wai yaushe zani hau gadon laushi? Mix kobincus Mafarki na
Writer(s): Sani Ahmad Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out