Credits

COMPOSITION & LYRICS
Nazir Haruna Maiatamfa
Nazir Haruna Maiatamfa
Songwriter

Lyrics

Kina yi mini kalamai Kina kira na da jarumai Rashin ki zaya saka ni Kullum na zubda hawaye Kina kashe ni da kauna Kina farantan raina Mai tabaki ko wanene Kawai Allah ya kiyaye Ni son ki yayi mini zane Yana ta yi mini iyo ne Kaman ruwan teku ne Gashi ya riki tani Baki sani baki sani damuwa A zuciyar ki tunda nayi karbuwa Zana miki, zana miki, zana miki Zana miki, zana miki garkuwa Tunda so ya zamo gamon jini Dana nufo ki sai ki kara kwarjini Bara nazo gare ki kinga gani ni Sai da ke zana more rayuwa Ra'ayin mu yazamo iri daya Har shigar mu ta zamo kala daya Kamar ruwan da dole sai da walkiya Kinga dole zamu kara shakuwa Kinai mini duk soyayya Don haka ban jayayya Gun ki akwai alkunya Gaki da tarbiya tawa Allah yayi mini kyauta Yau zan sada zumunta Don haka zan ririta Zan dauraye ki da soso Taka ce ni, na baka mukullin zuciyata Ko tsakanin mu ba'a shiga don bamu rata Bani kallan wanin ka yazo mini zuciya ta Sai da kai zan rayu In babu kai babu sauran kwana Zuciyata shiryu Ka zamo rai da numfashi na Zanyi imani, kan kaddarar so idan tazo min Zan cike buri kan son ka baiko idan har an min Ka zamo min sinadari kai zaka zamto uban 'ya'ya na (Maiatamfa on the Beat)
Lyrics powered by www.musixmatch.com
Get up to 2 months free of Apple Music
instagramSharePathic_arrow_out