Lyrics

Dawo dawo Kaine madubin dubawa kai nake ta duba Masoyi na ka dawo A'a bazan iya dake ba Tuba yau nakeyi laifina bazana sake yi ba Nidai bazana zo ba Kai hakuri ka tausayawa raina Lokuta da dama na duba ciki babu naki ki hakuri Um nayi maka laifi Gashi na gane kuskure na Na 'dauka da zafi Duniya ta wuce sanina In sake ta yafi, kaine zaka tallafan in zauna Eh eh magiya nakeyi, karkace bakayi dani ba Eh in har zaka dubani, madubi bazai maka 'karya ba Nidai bazana zo ba Kai hakuri ka tausayawa raina Tuba yau nakeyi laifina bazana sake yi ba Idan akwai dakika, ba wuya saika jarraba dama Allah ya taimake ka, yau da gobe sai kazam da girma Inka kore shakka, zabin Allah bai zama nadama Yanzu nayi nisa waiwayo kanki babu dama Masoyi na ka dawo A'a bazan iya dake ba Lokuta da dama na duba ciki babu naki ki hakuri Ka duba fassalina zan biyayya idan ka yarda Yanga tana gurina gani dakyau ko ban shafa hoda A'a'ah jan aji gurina, zana 'karashi yafi ma na da In kaki batu na zance Rabbi domin na fada Baka tausayi na kokwa kafiso in rasa raina Nidai bazana zo ba Kai hakuri ka tausayawa raina Tuba yau nakeyi lafina bazana sake yi ba Eh duka yaudara ne zancen nan naki na fahimta Babu so gabana ban kallonki ko kin canza fata Kujerar da na baki yanzu wata ce zaune akanta Mai kyau na hakika, wacce halinta ba mugunta Hakuri kiyo mani tarayya bazana yo dake ba Masoyi na ka dawo A'a bazan iya dake ba Lokuta da dama na duba ciki babu naki ki hakuri Eh na canza duka halina so nake ka gane Ko an bude zuciya ta cen cikinta kaine Kai kadai ne mai taimako na a duk cikin mutane Eh da zaki daina bina, to da kin gane Ban canza ra'ayi na kin bata lokaci ne Allah yayiman zabin kairi bazana 'bata raina ba
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out