Lyrics

Kana raina Eh, so ya kama ni kamar a mafarki Na zo sanar miki sai ki kula ni Kar ki guje mini amsa amo na So ya kama ka kamar a mafarki Na zo sanar maka sai ka kula ni Bana guje maka kaji amo na Nazo sanar miki dukka nufi na Abinda yanzu ya addabi rai na Tunda na kamu da son ki da kauna Na kasa yin tsaye ko na tsugunna Ki agaza mini tallafi rai na Ki yarda nayi miki kice matso guna So ya kama ka kamar a mafarki Na zo sanar miki sai ki kula ni Kar ki guje mini amsa amo na Mai zan fadi ka aminta da zance Ka yarda zuci da kai ta kadaice Komai kace mini zana amince Nidai bukata ta ka kudurce Idan zaman mu da kai ya kasance Toh ka zamo mai faranta rayi na So ya kama ni kamar a mafarki Na zo sanar maka sai ka kula ni Bana guje maka amsa amo na Indai da so a samu kulawa Gun kyautata miki bani gazawa Banda kamar ki Kudun da Arewa Sirrin cikin ciki yau na fitarwa Jira nake a gida ki sanarwa Ki mallaka min komai kina so na So ya kama ka kamar a mafarki Na zo sanar miki sai ki kula ni Kar ki guje mini amsa amo na So ya kama ni kamar a mafarki Na zo sanar miki sai ki kula ni Kar ki guje mini amsa amo na Lallai ko kayi abin a yaba ma Yarda a zuciya yau na aje ma Yau tuntuni zai daina matsa ma Domin a so yau nina tsaya ma A fuska ma in ka duba alama Toh zaka gamsu ka gane kana raina So ya kama ni kamar a mafarki Na zo sanar maka sai ka kula ni Bana guje maka kaji amo na Yau duniyar so tayi min fadi An min abinda a rai naji dadi Zan yayata a gari nayi kaudi Mahassadan mu a yau suka fadi Sai muyi raha mu kadai ta da tadi Dani dake mun aminta da juna So ya kama ka kamar a mafarki Na zo sanar maka sai ka kula ni Bana guje maka kaji amo na So ya kama ni kamar a mafarki Na zo sanar miki sai ki kula ni Kar ki guje mini amsa amo na So ya kama ka kamar a mafarki Na zo sanar maka sai ka kula ni Bana guje maka kaji amo na
Lyrics powered by www.musixmatch.com
Get up to 2 months free of Apple Music
instagramSharePathic_arrow_out