Lyrics

Jiya da yau, ha-ha-ha Yau da gobe, he-he-ha Jiya da yau mafarkin ki nake tayi cikin barci Yau da gobe sai Allah ina sauraro Jiya da yau mafarkin ka nake tayi cikin barci Yau da gobe sai Allah ina sauraro Jiya da yau mafarkin ki nake cikin barci na Munyi aure ni da ke, gamu mun zauna Kin yimin kwalliya fes, niko na zauna Ina kallon ki sarauniyar cikin mata Babu damuwa ko daya sanyi cikin rai na Nima haka take tamkar kana cikin zuciya Mafarkin ka yazo dole idan nayi kwanciya Da hoton ka nake tashi kullum safiya In kalle ka karin safe kenan sahibi Jiya da yau mafarkin ki nake tayi cikin barci Yau da gobe sai Allah ina sauraro Gimshiki na aure soyayya take sa wa, hoho Wadanda basu aure, su ake kira gwagware, hoho Tunda munyi niyya, mun zam sahun amare Alfa sai ka shirya, kar a ce ma tuzuru Jiya da yau, ha-ha-ha Yau da gobe, he-he-ha Jiya da yau mafarkin ki nake tayi cikin barci Yau da gobe sai Allah ina sauraro Kalma ta so sauraron ta nada dadi Ita ko kiyayya furucin ta babu dadi Zaman lafiya shike sa ayi nishadi Duba ina nishadi har tako na fadi Jiya da yau mafarkin ki nake tayi cikin barci Yau da gobe sai Allah ina sauraro Tambari na doka da sarewa na busawa Waka nake rerawa zo ki takawa Kwalliya nayo domin ke zana yi burgewa Dubi nima da turare na fesa Jiya da yau mafarkin ki nake tayi cikin barci Yau da gobe sai Allah ina sauraro Jiya da yau mafarkin ki nake tayi cikin barci (Jiya da yau mafarkin ka nake tayi cikin barci) Yau da gobe sai Allah ina sauraro (Yau da gobe sai Allah ina sauraro)
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out