Lyrics

Crown studio La baba, ga masu tashe Alhaji (na'am) Sai kayi rawa a nan (a gaban 'ya'ya na) Alhaji (na'am) Sai kayi rawa a nan (a gaban 'ya'ya na) Alhaji (iye) Sai kayi rawa anan (a gaban 'ya'yan nawa) Ahayye duniya budurwar wawaye Ahayye duniya budurwar wawaye Ye wayyo ni Allah Iye, iye, iyee wayyo ni Allah Ya Allah mai aradu mai turnaku, mai kwarankwatsi Allah mai wuta da aljana, sarkin kowa Ya Allah mai aradu mai turnaku, mai kwarankwatsi Allah mai wuta da aljana, sarkin kowa Gargadi zanyo ku bude kunnenku (Zango jamu za muje) Amma dai sai na kira shi sarkin mu (Zango jamu za muje) Ya zuljalalu wanda baka ba tasa (Zango jamu za muje) Sannan na girmama dan Amina manzon mu (Zango jamu za muje) Wanda ankayi duniya a domin sa (Zango jamu za muje) Iye rayuwa ta canza Mu so Allah da shi da manzo sa ai kunji yan uwa Ya Allah mai aradu mai turnaku, mai kwarankwatsi Allah mai wuta aljanna sarkin kowa Duniya gidan kashe ahu (Zango jamu za muje) Duniya rawa ta yan mata (Zango jamu za muje) Duniya tana da kyau tabbas (Zango jamu za muje) Gata kyakkyawa sanan budurwa ce (Zango jamu za muje) Idan ka bita ka shiga jahima (Zango jamu za muje) Wayyo zafi wutar Allah Sanan dadi aljanar firdausi kunji yan uwa Ya Allah mai aradu mai turnaku, mai kwarankwatsi Allah mai wuta da aljanna sarkin kowa Mutane duka basu san mutuwa (Zango jamu za muje) Amma kowa burin sa aljanna (Zango jamu za muje) Shugabani ma akwai na zalunci (Zango jamu za muje) Sanan wasu na kwanta adalci (Zango jamu za muje) Mutuwa bata barinka dan mulki (Zango jamu za muje) Wayyo koh karatun malam Wayyo Allah ko kudin alhaji kunji yan uwa Ya Allah mai aradu mai turnaku, mai kwarankwatsi Allah mai wuta da aljanna sarkin kowa Sabada, sabada, sabada, sabada Sabada, sabada, sabada, sabada Sabada, sabada, sabada, sabada Sabada, sabada, sabada, sabada Alhaji (na'am) Sai kayi rawa a nan (a gaban 'ya'ya na) Alhaji (iye) Sai kayi rawa anan (a gaban 'ya'ya nawa) Yeh Yeh Ka samu kudi kanata tinkaho (Zango jamu za muje) Ka hau mota kanata shan sauti (Zango jamu za muje) Ka dau chika kunata shan AC (Zango jamu za muje) Amman ka tina fah lahira dai daya ne (Zango jamu za muje) Sanan akwai wuta da aljana (Zango jamu za muje) Wayyo, wayyo zafi wutar Allah Ga dadi da rahamar Allah kunji yan uwa Ya Allah mai aradu mai turnaku, mai kwarankwatsi Allah mai wuta da aljanna sarkin kowa Alamun munafuki guda uku ne (Zango jamu za muje) Wurin zance yakan sako fariya (Zango jamu za muje) Idan yayi alkawar yakan saba (Zango jamu za muje) Idan an yarje dashi yaci amana (Zango jamu za muje) Munafurci yanzu ya zamo fashion (Zango jamu za muje) Wayyo muyo ibadun Allah Mu so Allah dashi da manzon sa kunji yan uwa Ya Allah mai aradu mai turnaku, mai kwarankwatsi Allah mai wuta da aljanna sarkin kowa Ni Adam Zango na rike Allah (Zango jamu za muje) Ni Adam Zango na rike rasululla (Zango jamu za muje) Ni Adam Zango na rike sallah (Zango jamu za muje) Sanna nabi uwata babu yin kwalla (Zango jamu za muje) Ina mai jifa? Ka jefa nuclear (Zango jamu za muje) Wayyo dogaro na Allah آيَة الْكُرْسِي zana jefa maka kaji makiyina Ya Allah mai aradu mai turnaku, mai kwarankwatsi Allah mai wuta da aljanna sarkin kowa Ya Allah mai aradu mai turnaku, mai kwarankwatsi Allah mai wuta da aljanna sarkin kowa Yeh Yeh Allah mai wuta da aljana, sarkin kowa (yeh) Sarkin kowa (yeh) Sarkin kowa
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out